Zaben Ekiti: Jonathan yayi wa shugaba Muhammadu Buhari nasiha mai ratsa zuciya

Zaben Ekiti: Jonathan yayi wa shugaba Muhammadu Buhari nasiha mai ratsa zuciya

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan mun samu cewa ya shawarci shugaban kasar Najeriya mai ci a yanzu Muhammadu Buhari da kar ya yi anfani da karfin mulkin sa wajen tankwara zaben jihar Ekiti da za'a gudanar.

Jonathan yayi wannan tsokacin ne yayin da yake gabatar da jawabin sa lokacin kaddamar da wata katafariyar gada a jihar Ekiti da gwamnan jihar Ayodele Fayose ya gina.

Zaben Ekiti: Jonathan yayi wa shugaba Muhammadu Buhari nasiha mai ratsa zuciya

Zaben Ekiti: Jonathan yayi wa shugaba Muhammadu Buhari nasiha mai ratsa zuciya

KU KARANTA: An soma korar karuwai daga garin Maiduguri

Legit.ng ta samu cewa Jonathan din yace yana so yayi anfani da wannan damar ya shaidawa shugaba Muhammadu Buhari cewa yayi kokari ya bar ra'ayin mutane ya bayyana wanda zai zama gwamnan jihar ta Ekiti.

A wani labarin kuma, Jami'an hukumar nan dake yake da cin hanci da rashawa a Najeriya ta EFCC dake a garin Fatakwal, jihar Ribas sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin kirista mai suna Fasto James Ezekiel bisa laifin damfara.

Kamar dai yadda muka samu, Fasto James Ezekiel din ya damfari wani mutum ne da sunan wai ya samo kwangilar Naira biliyan 1.8 don haka ne ma ya bukaci mutumin da ya bashi Naira miyan 1 da dubu dari 3 domin fitar da ita.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel