Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

Mun samu rahoton cewa Sufeto Janar na 'Yan sanda, Ibrahim Idris, ya bayyana dalilan sa na rashin amsa gayyatar majalisar dattawa.

Shugaban na 'yan sanda a yayin da ya nuna gazawar majalisar dattawa ya bayyana cewa, bayyanar sa a gaban majalisar ba ya da tushe ko wani muhimmin dalili face bukatar su ta karan kansu.

Ya ke cewa, muddin zai amsa kowace gayyata ta majalisar a karan kansa to kuwa hakan zai kawo nakasun lokaci na sauke nauye-nauyen da suka rataya a wuyan sa.

Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

Sufeton 'Yan sanda ya bayyana dalilin rashin amsa gayyatar Majalisar Dattawa

Babban sufeton na 'yan sanda ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin na kasar nan ta Najeriya ya ba shi dama na tura wakili da zai wakilce sa a yayin amsa kowace gayyata a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya yabawa Dangote dangane da Gudunmuwar Motoci 150 da ya bai wa Hukumar 'Yan sandan Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban na 'yan sanda ya bayyana wannan hujjoji da sanadin lauyan sa, Dakta Alex Izinyon cikin korafin da ya gabatar a babbar kotun tarayya dake garin Abuja.

Janar Idris cikin korafin sa ya bayyana cewa, majalisar ba ta da hujja ko ta sisin kobo wajen gayyatar sa dangane da harkallar dake tsakanin hukumomin tsaro na gurfanar da Sanatan jihar Kogi, Honarabul Dino Melaye a gaban Kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel