Babbar magana: Hukumar NDLEA ta lalata eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

Babbar magana: Hukumar NDLEA ta lalata eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

Kwamandan hukumar rundunar nan dake yake da safara tare kuma da shan miyagun kwayoyi ta tarayyar Najeriya watau National Dr*g Law Enforcement Agency, NDLEA a jihar Ondo mai suna Muhammad Sokoto ya sanar da samun nasarar bankado gonar wiwi mai girman eka 11,000.

Kamar dai yadda muka samu, Kwamandan rundunar a jihar ta Ondo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya ya kuma ce tuni dai hukumar ta lalata wannan gonar a tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2018.

Babbar magana: Hukumar NDLEA ta lalata eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

Babbar magana: Hukumar NDLEA ta lalata eka 11,000 ta gonar wiwi a wannan jihar ta Najeriya

KU KARANTA: Saraki, Kwankwaso da tawagar su za su koma PDP

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Imo dake a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki Rochas Okorocha ya bayyana cewa dole ne duk wani dan siyasa a Najeriya dole ne yayi sata sannan ya rayu saboda albashin su ba wani bane.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake fira da wakilin gidan talabijin din nan mai zaman kanta ta Channels ya bayyana cewa albashin gwamna a Najeriya Naira dubu dari bakwai ne kacal kuma baya isar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel