Cakuda garada da kananan yara: Majalisa zata titsiye shugaban gidajen yari na kasa

Cakuda garada da kananan yara: Majalisa zata titsiye shugaban gidajen yari na kasa

A ranar Laraba ne majalisar dattijai ta aike da sammaci ga shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa, Mista Ahmed Ja’afaru, domin yi mata bayanin dalilin da yasa ake cakuda cakuda kananan yara masu laifi da garada a gidajen yarin kasar nan.

Kazalika majalisar ta bukaci hukumomin tsaro dake kasar nan da su guji kama tare da tsare kananan, yara da suka aikata laifi, fiye da sa’o’i 48.

Gayyatar shugaban gidajen yarin na zuwa ne bayan mamba a majalisar, Sanata Victor Umeh daga jihar Anambra, ya gabatar da kudirin bukatar kare kananan yara masu laifi a zauren majalisar.

Cakuda garada da kananan yara: Majalisa zata titsiye shugaban gidajen yari na kasa

Shugaban gidajen yari na kasa, Ahmed Jafaru

Umeh ya bayyana cewar hankalin say a matukar tashi bayan ganin hotunan wasu kananan yara na gararamba cikin garada a cikin gidajen yari a shafi na 13 zuwa 15 a jaridar The Nation ta ranar 31 ga watan Maris.

Dan majalisar ya bayyana cewa’yan sanda na kara shekarun yaran kafin gurfanar das u a gaban kotu tare da yaudarar yaran cewar idan ba a kara masu shekaru ba kotu ba zata wanke su daga laifin da suka aikata ba.

DUBA WANNAN: An sace miliyoyin kudin da za a biya ma'aikatan wata karamar hukuma a jihar kebbi albashi

Kazalika, Sanata Umeh ya nuna damuwar sa bisa tsare jarirai tare da iyayen su mata a gidajen yari, yana mai bayyana hakan da cewar zai gurbata tunanin yaran.

‘Yan majalisar sun amince da bukatar Umeh ta yin dokar da zata tabbatar an daina cakuda garada da kananan yara tare da shiga da jarirai gidajen yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel