Kasar Denmark ta haramta wa mata Musulmai saka nikabi a bainar jama'a

Kasar Denmark ta haramta wa mata Musulmai saka nikabi a bainar jama'a

Kasar Denmark tayi na'am da dokar hanawa mata saka nikabi a cikin bainar jama'a.

'Yan majalisar dokokin kasar ne suka yarda da kudurin haramcin, da za a fara amfani da shi a watan Agusta mai zuwa.

Wannan doka na haramtawa mata sanya nikabi ya samu karbuwa a kasashen Turai da dama .

Duk matar da aka samu ta lullube fuska da sunan nikabi za a ci ta tarar dala 160 a kasar ta Denmark.

Kudin tarar kan iya ninkaya idan aka sake samun mace da sake aikata laifin.

Kasar Denmark ta haramta wa mata Musulmai saka nikabi a bainar jama'a

Kasar Denmark ta haramta wa mata Musulmai saka nikabi a bainar jama'a

Ko da yake, dokar ba ta ambaci matan musulmai ba, amma ta ce, "duk wanda aka kama ya yi amfani da wani mayafi da ya rufe fuska a bainar jama'a za a ci tarar shi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Zan azurta ku da miliyoyi idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wata yar Najeriya ta dauyin taimakawa Musulmai a wannan lokaci na Ramadana.

Idan ka na da shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku tuntubi shafukanmu: https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel