Na kwashe shekaru da dama ina tara kudin da na siyawa matata motar G-Wagon a matsayin kyauta - Gbajabiamila

Na kwashe shekaru da dama ina tara kudin da na siyawa matata motar G-Wagon a matsayin kyauta - Gbajabiamila

- Femi Gbajabiamila, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ya maida martini ga sukar da ake game da kyautar da ya baiwa matarsa a zagayowar ranar haihuwarta

- Kwanan nan ya ba matarsa kyautar motar G-Wagon domin murnr cikarta shekara 50 a duniya

- Dan majalisan tarayyan ya bayyana cewa ya kwashe tsawon shekaru da dama yana tara kudi domin siyawa matarsa motan

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya kare kansa akan korafi da ake tayi game da motar da ya ba matasa kyauta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dan majalisan yayi tashe a shafukan zumunta tsakawon kwanaki bayan wani hoto da bidiyo sun billo inda ya mallakawa matarsa motar Benz G-Wagon sabuwa fil.

Na kwashe shekaru da dama ina tara kudin da na siyawa matata motar G-Wagon a matsayin kyau - Gbajabiamila

Na kwashe shekaru da dama ina tara kudin da na siyawa matata motar G-Wagon a matsayin kyau - Gbajabiamila

Legit.ng ta tattaro cewa dan majalisan ya gabatar da kyautar banmamakin ne a ranar 27 ga watan Mayu yayinda uwargidan tasa ta cika shekara 50 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Kalli hotunan manyan jaruman Kannywood 5 da suka tafi kasa mai tsarki don yin ibadah a wannan watan na Ramadan

Da yake maida martani a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu, Gbajabiamila yace ya tara kudin ne tsawon shekaru domin siyawa matarsa tsadadden motan.

Yace kamata yayi gabatar mata da motan ya kasance lamari na cikin gida. Amma a lokacin da motar ya iso baki sun rigada sun hallara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel