‘Yan fashi sun kwace miliyoyin da za biya ma’aikatan wata karamar hukuma albashi a jihar Kebbi

‘Yan fashi sun kwace miliyoyin da za biya ma’aikatan wata karamar hukuma albashi a jihar Kebbi

Wasu da ake zargi ‘yan fashi ne sun yi awon gaba da kudi, miliyan N9m, da za a biya ma’aikatan karamar hukumar Gwandu dake aiki a sashen lafiya da na noma albashi.

Shugaban karamar Gwandu, Shehu Bagudu, ya shaidawa manema labarai a yau, Alhamis, cewar lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Mayu.

Ya kara da cewar lamarin ya faru ne bayan da kashiyan karamar hukumar ya karbo kudin daga banki ya kai gidan sa.

‘Yan fashi sun kwace miliyoyin da za biya ma’aikatan wata karamar hukuma albashi a jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu

A yayin da yake kokarin bude kofar gidan sa sai wasu da yake kyautata zaton sun biyo shi daga banki ne suka afka masa tare da kwace motar sa da ya dauko kudin albashin ma’aikatan a ciki. Amma daga baya an samu motar a karamar hukumar Tambuwal dake jihar Sokoto,” a cewar Bagudu.

DUBA WANNAN: Kachikwu ya bayyana cewar zai ajiye aikin sa

Kazalika shugaban karamar hukumar ya ce ba wai yana kare kashiyan ba ne saboda surukin sa ne tare da bayyana cewar ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike.

Surukina ne tun ban san zan zama shugaban karamar hukuma ba kuma kowa ya san mutum ne dake da riko da amana,” shugaban karamar hukumar ya bayyana.

Bagudu ya ce sun rubutawa ma’aikatar kula da kananan hukumomi abinda ya faru kuma suna zaman dakon amsar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel