Karamin ministan man fetur Kachikwu zai ajiye aikin sa

Karamin ministan man fetur Kachikwu zai ajiye aikin sa

Karamin ministan man fetur na kasa, Dakta Emmanuel Ibekachikwu, ya bayyana cewar zai ajiye mukamin sa idan ya kasance cewar kasha 80% na matatun man fetur din mu na gida basa aiki zuwa karshen shekarar 2019.

Kachikwu ya bayyana hakan da safiyar yau, Alhamis, yayin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels dake birnin tarayya, Abuja.

Kachikwu ya kara da cewar yanzu haka za a iya cewa an kamala gyara da kuma inganta matatun man fetur na cikin gida domin habaka kasuwancin man fetur da albarkatun sa a Najeriya.

Karamin ministan man fetur Kachikwu zai ajiye aikin sa

Karamin ministan man fetur Kachikwu

Ko a kwanakin baya saida Kachikwu ya shaidawa manema labarai cewar gwamnatin Najeriya tayi nasarar jawo hankalin masu zuba jari a harkokin da suka shafi kasuwancin sinadarin man fetur.

A baya, Kachikwu ya taba furta cewar gwamnati na duba yiwuwar tilsatawa manyan kamfanonin man fetur dake kasar nan gina matatun mai a Najeriya.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ba zai fadi zaben 2019 ba - Fadar shugaban kasa

Ministan ya bayyana cewar tilas Najeriya ta zama babbar kasar da za a ke sayen tataccen daga wurin ta tare da bayyana hakan a matsayin mafitar da kasar ke da ita.

Yin hakan a cewar Kachikwu zai samar da aiki ga matasa da kuma bunkasa tattalin arzikin ta hanyoyi da dama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel