Zaben 2019: Shugaban Kasa Buhari ya ba Matasa shawara su tari wani jikon

Zaben 2019: Shugaban Kasa Buhari ya ba Matasa shawara su tari wani jikon

- Shugaba Buhari ya sa hannu a kudirin “Not Too Young To Run” dazu nan

- Yanzu Matasa sun samu daman tsayawa takarar Shugaban Kasa a Najeriya

- Sai dai Buhari yace Matasan su hakura da mulki har sai bayan zaben 2019

Mun samu labari dazu daga Jaridar Daily Trust cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fadawa Matasan Kasar nan su hakura da neman takarar shugaban Kasar nan a zabe mai zuwa na 2019.

A yau ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kudirin da za ta ba Matasa damar shigowa cikin harkar takara a Kasar a Fadar Aso Villa. Yanzu dai ya halarta a cikin dokar Kasar ‘Dan shekara 25 ya fito kujerar ‘Dan Majalisa.

KU KARANTA: Buhari ya rattaba hannu kan kudirin ba Matasa daman takara

Sai dai bayan sa hannu a kan kudirin na “Not-Too-Young-To-Run”, Shugaban Kasar ya fadawa Matasan Kasar su hakura da takarar Shugaban Kasa har sai bayan zaben 2019. Ana tunani yanzu Matasa za su fara harin kujerar Shugaban Kasar.

Shugaban Kasar mai shekara 74 a Duniya yana sa ran zarcewa kan kujerar Shugaban Kasa bayan 2019. Ba mamaki ne don haka Shugaban yace Matasan su daina tunanin samun mulkin Kasar har sai bayan 2019 zuwa lokacin Buhari yayi wa’adi 2.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel