Gwamnatin jihar Kaduna na shirya rusa min gida – Sanata Hunkuyi ya kawo kuka

Gwamnatin jihar Kaduna na shirya rusa min gida – Sanata Hunkuyi ya kawo kuka

Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa a majalisan dattawan tarayya, Suleiman Otthman Hunkuyi, ya kawo kukansa kan shirin da gwamnatin jihar Kaduna karashin gwamna Nasir El-Rufa’I ke yin a rusa masa gidan da yae zaune a jihar Kaduna.

Sanatan ya ce gwamnatin ta lashi taobin rusa gidansa duk da cewa kotu ta bada umurnin hana hakan. Ya bayyana wannan abu ne a shafinsa na Facebook inda yace:

“Gwamnatin jihar Kaduna na shirin rusa min gida duk da hukuncin kotu. Har yanzu wannan batu na tsugunne a babban kotun jihar Kaduna amma gwamnati ta rantse sai ta aikata wannan zalunci.

“Wannan na daga cikin umurnin kotun da gwamnatin jihar Kaduna ke sabawa. Mun san da hakan a jihar Kaduna saboda suna ganin sun fi karfin doka...”

KU KARANTA: Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

Wannan shine karo na biyu da za’a rusawa wannan sanatan gida a jihar Kaduna. A kwanakin baya, gwamnatin jihar a rusa masa gidansa da ke Plot 11B, Sambo Close, Angwan Rimi Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel