Yanzu Yanzu: Buhari ya rattaba hannu a dokar ba matasa damar shiga siyasa (bidiyo)

Yanzu Yanzu: Buhari ya rattaba hannu a dokar ba matasa damar shiga siyasa (bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar rage shekarun takara wato 'Not Too Young to Run' a yau Alhamis, 31 ga wata Mayu.

Hadimin shugaban kasa na musamman, Bashir Ahmad ya bayyana hakan a shafin twitter.

Dama a baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasar yayi alwashin amincewa da dokar nan da zata bawa matasa damar fitowa a dama dasu a siyasa wato "Not Too Young to Run" a turance.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanata Dino Melaye ya bukaci ban-hakuri daga shugaba Buhari kan zagin da akayiwa majalisa

Shugaban kasar ya bayyana hakan a wurin bikin tunawa da ranar dimokradiyya da aka gabatar a babban birnin tarayya Abuja a ranar 29 ga watan Mayu.

Sannan kuma ya bukaci dukkan 'yan Najeriya dasu so junan su da amana, sannan kuma suyi kokarin ganin sun zauna lafiya da juna.

Shugaban kasar ya bukaci 'yan Najeriya dasu bada hadin kai da goyon baya, domin ganin an gabatar da zabe cikin lumana da kwanciyar hankali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel