Majalisa ta ki tantance wani mutum da Buhari ya tura, ta bayar da dalilin ta

Majalisa ta ki tantance wani mutum da Buhari ya tura, ta bayar da dalilin ta

- Majalisar dattawa ta amince da mutane hudu cikin biyar da shugaba Buhari ya aike musu a matsayin mambobin direktocin CBN

- A cewar majalisar, daya daga cikin mutanen da shugaba Buhari ya aike, Dr. Abdu Abubakar bai cika wasu ka'idoji na dattaku ba

- Majalisar ta ce Abubakar bai bayar da gamsasun amsoshi a kan wasu tambayoyi da akayi masa ba

Hudu da cikin mutane biyar da shugaba Buhari ya aike wa majalisa don amincewa da su a matsayin direktocin marasa cikakun iko a babban bankin Najeriya CBN sun amincewar majalisar.

Wadanda aka amince da su sun hada da Ummu Jalingo, Justitia Odinakachukwu, Mike Obadan da Adeola Adetunji.

Legit.ng ta gano cewa shugaban majalisa Bukola Saraki ya ce majalisar ta mika Dr. Abdu Abubakar zuwa ga kwamitin harkokin banki domin su kara zurfafa bincike a akansa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Majalisa taki tantance wani mutum da Buhari ya tura

Majalisa taki tantance wani mutum da Buhari ya tura

KU KARANTA: Liverpool da Madrid: Allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumi - Malamin Islama

Sanata Saraki ya mika sakon taya murna ga mutane hudun da suka samu amincewar majalisar kana ya bukace su da su cigaba da bayar da gudunmawarsu wajen cigaban tattalin arzikin Najeriya.

Ciyaman din kwamitin majalisar, Rafiu Adebayo, ya ce: "Wadanda aka tantance suna da ilimi sosai kan dokokin CBN. Kuma kotun da'ar ma'aikata da sauran hukumomin tsaro sun tantance su. Sai dai daya daga cikin wanda aka tantance, Dr. Abdu Abubakar ya fadi jarabawar da kwamitin saboda kwamitin bata gamsu da irin amsoshin da ya bayar ba hakan yasa bai cika ka'idojin kasancewa a CBN din ba."

A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar dattawa sunayen mutane biyar da ya ke bukata a amince da su a matsayin direktoci marasa cikakun iko a CBN.

A cewar mai bawa shugaba shawara na musamman a kan kafafen yada labarai, Femi Adesina, shugba Buhari ya aike da sunayen ne a wata wasika da ya aike wa shugaban majalisa Bukola Saraki a ranar Laraba 12 ga watan Afrilun 2017.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel