Wani Fasto ya roki mabiyan sa dasu taimaka su saya masa jirgin sama na hudu

Wani Fasto ya roki mabiyan sa dasu taimaka su saya masa jirgin sama na hudu

Wani Faston addinin kirista dan kasar Amurka wanda ya mallaki jiragen sama har guda uku ya bukaci taimako a wurin mabiyanshi don su siya mishi jirgin sama na hudu

Wani Fasto ya roki mabiyan sa dasu taimaka su saya masa jirgin sama na hudu

Wani Fasto ya roki mabiyan sa dasu taimaka su saya masa jirgin sama na hudu

Wani Faston addinin kirista dan kasar Amurka wanda ya mallaki jiragen sama har guda uku ya bukaci taimako a wurin mabiyanshi don su siya mishi jirgin sama na hudu.

Fasto Jesse Duplantis yace ubangiji yayi mishi wahayi, inda ya umarce shi da ya siya Falcon 7X, wanda kudin shi yakai kimanin dala miliyan 54.

DUBA WANNAN: PDP: Kabiru Turaki ya zabi Boni Haruna a matsayin shugaban yakin neman zabensa na shugaban kasa

Ya kara da cewa ya jinkirta siyan jirgin da farko amma sai ubangiji ya kara yi mishi wahayi yake fada mishi cewa: "Bance ka siya da kudin ka ba, ka yarda da hakan kawai."

Duk da dai masu da'awa da suka mallaki jirgin kansu kadan ne, wannan maganar ta jawo cece ku ce.

Masu amfani da shafin yanar gizo na Twitter sun maida martanin rashin yarda, da yawansu suna jawo ayoyi daga Bible da suke hani akan son kai da makaryatan malamai. Wasu kuma suna cewa gara ayi amfani da kudin don tallafawa marasa hali.

A wani bidiyo da yasa a shafin shi na yanar gizo, Mista Duplantis mai shekaru 68 a duniya yayi bayani kamar haka: "Kunsan na mallaki jiragen kaina a lokuta daban daban har sau uku, kuma nayi amfani dasu wurin bautawa ubangiji Yesu."

"Yanzu, wasu mutane basu yarda fastoci su mallaki jirgin kansu ba. Na yarda da cewa fastoci suna amfani da duk dukiyar su da karfin su don daukaka kira zuwa gaskiya."

A lokacin da yake tsaye kusa da jirgin na shi na yanzu, yace jirgin da ya siya shekaru 12 da suka wuce baya amfani dashi saboda baya iya yawo duk inda yake so dashi, ma'ana baya iya siyan man jirgin.

A wani hoto kuma da aka bayyana a bidiyon nashi, ya nuna faston a tsaye a gaban jirage guda 3 da rubutu kamar haka: "Bawai don mallaka ba ne, don fifiko ne."

Mista Duplantis yace Yesu ya sanar dashi cewa "Ka shiga duniya ka yada kalmar ubangiji ga kowane halitta, yanzu ya zamuyi? Bazan yi doguwar rayuwar da zan dinga tafiya a mota ba ko jirgin ruwa ko jirgin kasa, amma zan iya a jirgin sama."

A 2015, Mista Duplantis ya bayyana a wani bidiyo shi da wani fasto, Kenneth Copeland, a inda Mista Copeland ya misalta tafiya a jirgin sama na haya da "Doguwar tafiya tare da shaidanu."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel