Idanun wani Lebura da ya casa Dansanda sun raina fata bayan da Kotu ta yanke masa hukunci

Idanun wani Lebura da ya casa Dansanda sun raina fata bayan da Kotu ta yanke masa hukunci

Wata Kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a garin Minna ta yanke ma wani matashin Lebura, Saminu Abdulrahim hukucin zaman gidan kaso na tsawo watanni bakwai, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

An gurfanar da Leburan ne a gaban Kotu sakamakon lakada ma wani Dansanda dukan tsiya a bakin aiki, da wannan ne ake tuhumar Leburan da laifuka da suka hada da cin zarafin Dansanda da kuma yi masa barazana.

KU KARANTA: Don na ceto Najeriya ba don bukatar kashin kai nake son zama shugaban kasa ba – Atiku

Dansanda mai shigar da kara, Inspekta Cletus Ibrahim ya bayyana ma Kotu cewa Lebura ya lakada ma wani Dansandan Sajan Mustapha Abdullahi dukan tsiya a ranar 29 ga watan Mayu, a lokacin da yake bakin aiki a wata Kotun shari;ar Musulunci dake Kpakungu.

Idanun wani Lebura da ya casa Dansanda sun raina fata bayan da Kotu ta yanke masa hukunci

Kotun Musulunci

Dansandan ya bayyana ma Kotu cewa laifin da Leburan ya aikata ya saba ma sashi na 265 da 397 na kundin hukunta manyan laifuka, don haka ya yi kira ga Kotu ta yi duba da sashi na 157 na kundin ta hukunta wanda ake zargin.

Sai dai wanda zargin ya amsa laifinsa, inda ya roki Kotu da ta masa sassauci, kamar yadda shi ma lauyansa, Abubakar Danladi ya roki Kotu, inda ya bayyana mata cewa wannan ne karo na farko da Leburan ya aikata irin wannan laifin, kuma bai wahalar da Sharia ba.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai Alkali Ahmed Bima ya yanke ma Lebura hukuncin zaman gidan kaso na tsawon watanni biyu bisa tuhuma ta farko, ko ya biyar tarar kudi naira dubu biyar, yayin da tuhuma ta biyu kuwa ya yanke masa watanni biyar a Kurkuku ko biyan taran naira dubu goma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel