Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar Olisa Metuh

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar Olisa Metuh

Wata babban kotun Abuja da ke zamanta a Maitama ta tsayar da ranar Alhamis 11 ga watan Yuli a matsayin ranar da za ta yanke hukunci a kan bukatar da tsohon mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Olisah Metuh ya shigar na neman kotu tayi watsi da tuhumar da ake masa.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ne ta gurfanar da Metuh a kotu a watan Janairun shekarar 2015 bisa aikata laifuka biyu wadanda ke da alaka da lalata shaida.

KU KARANTA: Allah ne ya hukunta Salah saboda kin yin azumu - Malamin Islama

An dage shari'ar da ke gaban Alkali Ishaq Bello har zuwa ranar 11 ga watan Yuli bayan tattaunawa da lauyoyi. A baya an taba dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Mayu don yanke hukunci a kan bukatar Metuh na fatali da karar.

Kotu ta saka ranar da za'a yanke hukunci a shari'ar Metuh

Kotu ta saka ranar da za'a yanke hukunci a shari'ar Metuh

Lauyan Metuh, Onyechi Ikpeazu (SAN) ya shaidawa kotu a ranar 10 ga watan Octoba cewa sun shigar da bukatarsu na cewa Metuh bashi da wata tambaya da zai zo ya amsa a gaban kotu.

A yayinda da ya ke kare bukatarsa, Mr Ikpeazu ya shaidawa kotu cewa masu tuhumar Metuh basu gabatar da wasu gamsasun dalilai da zai sa wanda ya ke karewa ya hallarci kotu don amsa wasu tambayoyi ba.

Ya kuma kara da cewa dokar kasa ta bawa Metuh damar kin furta magana ko janye duk wata magana da ya furta ko rubuta a yayinda ya ke bayar da bayaninsa ga hukuma.

Mr Ikpeazu ya kuma ce Metuh na da ikon janye wani sashi na cikin abinda ya rubuta ba tare da an tursasa masa ba.

Sai dai lauyan EFCC Mr Tahir ya ce janye kalaman da wanda ake tuhuma daban ya ke da lalata takardan da aka rubuta shaidar, ya kuma roki kotun ta bukaci Metuh ya gurfanar gabanta don amsa tambayoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel