Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

- Ana cigaba da samun gagarumar nasara a cigaba da yaki da kungiyar Boko Haram

- Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani yanki na jihar da yake hannun ‘yan tada kayar baya na Boko Haram

Gwamna Shettima ya ce duk cewa yanzu Boko Haram basa rike da wani yanki a jihar, amma duk da haka mayakan na kai hare-hare sai dai basu taka kara sun karya ba, saboda kokari da Sojoji da kuma sauran Jami’an tsaro keyi wajen dakile duk wani yunkuri na ‘yan Boko Haram din.

Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

Ya ce ya kamata yayi a jinjinawa Jami’an tsaro a bisa kokarin da suke a jihar ta Borno da ma yanki Arewa maso Gabas baki daya.

KU KARANTA: Hotunan Buratai da Ambode yayin bude wata sabuwar barikin sojoji a Legas

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da Mukkadashin Kakakin Sojin rukuni na 7 na Sojin kasar ya kai masa ziyara wato Birgediya Janar Abdulmalik Biu, a fadar gwamnatin jihar dake Maiduuguri.

Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

Kuji ku kara ji, babu wani yanki na Borno da yake karkashin ikon Boko Harama – Shettima

“Shekaru hudu da suka wuce mun samu kanmu a cikin mummunan hali wanda a sanadin hakan yasa duk wasu hanyoyi da suka hada jihar mu da wasu garuruwa aka rufe su. Amma bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yunkurin Jami’an tsaro na kasar nan yanzu haka komai ya dawo daidai, ba abinda zamu ce sai dai mu ce muna matukar farin ciki da samun shugaba Muhammadu Buhari”.

Ya bayyanawa sabon mukkadashin cewa a matsayinsa na dan kasa na gari zai cigaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an cigaba da samun nasara da kuma kawo karshen duk wani tashin hankali a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel