Ashe suna nan: ‘Yan sanda sun kama ‘yan kungiyar a-ware ta IPOB yayin zanga-zanga a Enugu

Ashe suna nan: ‘Yan sanda sun kama ‘yan kungiyar a-ware ta IPOB yayin zanga-zanga a Enugu

Jami’an ‘yan sanda sun kama mambobin haramtacciyar kungiyar ‘yan a-ware ta IPOB yayin da suke gudanar da zanga-zanga a Enugu.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Danmallam Mohammed, ya tabbatar da kama ‘yan kungiyar ta IPOB yayin da suke zanga-zanga a gaban gidan gwamnatin jihar Enugu, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

An sanar da ni cewar wasu ‘yan kungiyar IPOB da kuma ‘yan Biyafra na gudanar da zanga-zanga a gaban gidan gwamnatin jihar Enugu kuma ba tare da bata lokaci ni da jami’ai na muka isa wuri muka kama su,” a cewar kwamishina Danmalam.

Ashe suna nan: ‘Yan sanda sun kama ‘yan kungiyar a-ware ta IPOB yayin zanga-zanga a Enugu

‘Yan kungiyar a-ware ta IPOB yayin zanga-zanga

Daga cikin wadanda aka kama akwai Benjamin Onwuka wanda kwamishinan y ace ya taba kasha jami’in dan sanda yayin wata zanga-zangar kungiyar IPOB a shekarar 2014.

Kungiyar IPOB ta bayar da umarnin zama a gida a jiya, Laraba, 30 ga watan Mayu, ga duk ‘ya’yan ta dake fadin Najeiya, umarnin da gwamnatoci suka ce zasu dauki mataki a kan duk wanda ya yi biyayya.

DUBA WANNAN: Su waye suka karkatar da dabinon fiye da miliayan N20m da kasar Saudiyya ta aikowa Musulman Najeriya?

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar ‘yan kasuwa a Kalaba sun yi burus da umarni kungiyar ta IPOB.

Wasu rahotanni sun bayyana cewar ‘yan kungiyar ta IPOB sun yi ikirarin cewar, zasu kwace gidan gwamnatin jihar Enugu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel