Ana Fafutikar Ceto 'Yan Matan Chibok da 'Dalibar Dapchi ta 'Karshe - Hukumar Sojin Kasa

Ana Fafutikar Ceto 'Yan Matan Chibok da 'Dalibar Dapchi ta 'Karshe - Hukumar Sojin Kasa

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar sojin kasa ta Najeriya ta bayyana cewa, tuni ta fantsama cikin shirin ceto ragowar 'yan Matan Chibok da kuma dalibar Dapchi ta karshe, Leah Sharibu, da ke tsare a hannun 'yan ta'adda na Boko Haram.

Wani babban dakarun sojin, Manjo Janar Attahiru Ibrahim, shine ya bayyana hakan a yayin wani shiri da kafar watsa labarai ta NTA, inda ya bayar da tabbacin cewa sauran kiris Leah Sharibu da ragowar 'yan matan Chibok su sadu da ahalin su.

Manjo Ibrahim wanda ya kasance tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole ya bayyana cewa, yana da kyakkyawan zato dangane da kokarin da dakarun sojin ke gudanarwa a halin yanzu wajen ceto 'yan Matan da suka shafe tsawon lokuta a hannun 'yan ta'adda.

Ana Fafutikar Ceto 'Yan Matan Chibok da 'Dalibar Dapchi ta 'Karshe - Hukumar Sojin Kasa

Ana Fafutikar Ceto 'Yan Matan Chibok da 'Dalibar Dapchi ta 'Karshe - Hukumar Sojin Kasa

A ranar talatar da ta gabata ne wasu kungiyoyi biyu masu kare hakkin dan Adam suka huro wuta kan shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakamakon kame bakin sa da yayi dangane da batun Leah Sharibu da ragowar 'yan matan Chibok cikin jawaban sa na tunawa da ranar Dimokuradiyya.

KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero

Dangane da batun rikicin makiyaya da manoma a cikin shirin na gidan Talabin ta kasa, hukumar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta kaddamar da wasu cibiyoyin kawo dauki na gaggawa a jihohin da abin ya fi shafa da suka hadar da Nasarawa, Benuwe da kuma Taraba.

Kakakin hukumar, Air Vice Marshal Olatakunbo Adesanya, ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar ta dauki sabbin dakaru 7,000 cikin shekaru uku da suka gabata domin inganta harkokin ta na gudanarwa da bunkasa tsaro a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel