Har yanzu gwamnatin Najeriya bata hukunta kowa ba dangane da batan kyautar dabinon Saudiyya

Har yanzu gwamnatin Najeriya bata hukunta kowa ba dangane da batan kyautar dabinon Saudiyya

Shekara guda bayan karkatar da kyautar ton 200 na dabino da gwamnatin kasar Saudiyya ta bayar domin rabawa masu azumi marasa galihu, har yanzu gwamnatin Najeriya bata bankado ko bayyana mutanen dake da hannu cikin wannan badakala ba.

Kasar Saudiyya ta damkawa hukumomin Najeriya dabinon ne domin rabawa ga mutanen dake zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da kuma masallatai.

Saidai abin haushi, dabinon ya kare a shagunan ‘yan kasuwa da wurin ‘yan talla a titunan jihohin Najeriya musamman Abuja da Borno. Hukumomi basu raba dabinon kamar yadda hukumar Saudi ta umarta ba.

Har yanzu gwamnatin Najeriya bata hukunta kowa ba dangane da batan kyautar dabinon Saudiyya

Dabino

Dabino na da matukar muhimmanci wajen bude baki ga masu azumi kamar yadda addinin Islama ya fada a cikin litattafai.

Gwamnatin Najeriya ta aike da takardar neman afuwar kasar Saudiyya bisa abinda ya faru tare da daukan alkawarin binciko masu hannu cikin badakalar karkatar da dabinon domin hukunta su.

DUBA WANNAN: Noma tushen arziki: Hotunan gonar gwamna Shettima da garken Shanun sa

Karamar ministar harkokin kasar waje, Khadija Abba Ibrahim, ta bayyana cewar ba a yi amfani da dabinon ta hanyar da ya kamata ba, sannan ta bayar da hakuri a kana bin kunyar da ya faru.

Saidai wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa ya ce ma’aikatar harkokin kasashen waje tayi kunnen uwar shegu bayan tuntubar ta a kan matsayin binciken karkatar da dabinon.

Kazalika jaridar ta ce ton 200 na dabinon da kasar Saudi ta bayar yana da daraja a kasuwa da ta kai na kimanin miliyan N20m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel