Jama’ar unguwa sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun kona motarsu sanadiyar kisan dan achaba

Jama’ar unguwa sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun kona motarsu sanadiyar kisan dan achaba

Rikici ya barke ranan Laraba, 30 ga watan Mayu a Ibeshe, unguwar Ikorordun jihar Legas yayinda yan achaban unguwa sun kai farmaki ofishin yan sandan sukayi musu ruwan duwatsu da kwalabe kuma sukayi kokarin kona ofishin.

Jaridar Punch ta samu labarin cewa basu samu damar kona ofishin yan sandan ba sanadiyar harbe-harben bindigan da yan sanda sukayi domin tarwatsa jama’ar.

Bayan haka, yan babur din suka bankawa motan yan sandan wuta kuma suka suburbudi duk dan sandan da suka gani.

Dan babur din da kashe ma suna Paul yam utu ne da safiyar asabar bayan wani hadari da ya samu sakamakon tsareshi da yan sanda suka kokarin yi.

Jama’ar unguwa sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun kona motarsu sanadiyar kisan dan achaba

Jama’ar unguwa sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun kona motarsu sanadiyar kisan dan achaba

KU KARANTA: Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

Wata mata wacce aa sakaye sunanta ta bayyana cewa dan achaban ya yi kokarin tserewa yan sandan ne kawai sai tsaytsayi ta hau kansa yayi hadari.

Tace: “Mutumin na dauke da fasinja ranan Talata sai yayi arangama da yan sanda. Yayinda yake kokarin tserewa sai ya fada kwata. Sai yan sandan suka bishi har cikin kwatamin.

“Maimakon sun kaishi asibiti, sai suka dauke babur dinsa suka barshi cikin kwatan yam utu.

“Daga baya wani abokinshi ya kai shi asibiti inda yam utu sa safen nan (Laraba)."

Wani mazani ya bayyana cewa ba da dadewa ba marigayi ya rasa mahaifiyarsa da uwargidansa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel