Yan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Yan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Gwamnan ihar Zamfara, Abdulaziz Yari, da takwaran shi na jihar Jigawa, Abubakar Badaru sun tarbi masu sauya sheka da dama daga jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Jigawa.

Yari ya kasance a jihar Jigawa domin yaba ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar kwanakin baya.

A baya PDP ta bayyana ziyarar da shugaban kasa Buhari ya kai jihar Jigawa a matsayin abun dariya. Sunce ayyukan da shugaban kasar ya kaddamar basu cancaci ambato ba.

Amma shugaba Buhari yace ayyukan na da yawa sannan shugaba kasar bai wadataccen lokacin kaddamar da su.

Yan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Yan PDP da yawa sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Taron wanda aka gudanar a karamar hukumar Jahun na jihar ya samu kaddamar da hanayr garin ahun da kuma na Gagarawa Bosowa.

KU KARANTA KUMA: Na yafewa Kwankwaso da mabiyansa yan Kwankwasiyya - Ganduje

A wajen taron shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Kiri ya yabama shugaban masu sauya shekar, Ibrahim Aujara bisa ga jagorantar masu sauya shekar da yayi a kokarinsu na sauya katinsu na PDP zuwa na APC.

Mista Kiri yayiwa masu sauya shekar alkawarin samun daidaito a jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel