IMF: Za mu iya biyan duk bashin da ke kan mu – Ministar kudi

IMF: Za mu iya biyan duk bashin da ke kan mu – Ministar kudi

- Gwamnatin Buhari tace Najeriya na iya biyan duk tarin bashin da ke kan ta

- Kwanaki mun ji cewa hankalin I.M.F ya tashi kan bashin da Najeriya ke ci

- Sai dai Ministar kudin kasar tace sam babu abin tada hankali kan Najeriya

Mun samu labari cewa Ministar kudi ta Najeriya Kemi Adeosun tace hankalin Hukumar lamuni ta Duniya watau IMF bai tashi ba game da makukun bashin da ke kan Najeriya na Tiriliyan 21.7.

IMF: Za mu iya biyan duk bashin da ke kan mu – Ministar kudi

Bashin da ake bin Najeriya ya karu a lokacin Buhari

Jaridar Punch ta rahoto Ministar Kasar tana cewa Najeriya na iya biyan duk bashin da ke kan ta. Misis Kemi Adeosun tace inda aka duba bashin Kasar da kuma karfin tattalin arzikin Najeriya za a ga cewa bashin ma ba wani mai yawa bane.

KU KARANTA: Aliko Dangote ya bayyana babban burin sa a Duniya

Ministar ta karyata cewa IMF ta na ganin cewa zai yi wahala Najeriya ta iya biyan tarin bashin da ke kan ta. Adeosun tace ko kadan babu wani abin damuwa domin bashin da ake bin Najeriya yana cikin mafi karanci a kaf kasashen Afrika.

An samu bashin sanadiyyar ratar da ke cikin kasafin kudin kasar ne kuma Ministar ta kudi tace ana kokarin ganin an rage karbar bashin a Duniya. Adeosun ta ka cewa an ci bashi ne domin ayi wa Najeriya aikin da zai yi amfani har nan gaba.

Kemi Adeosun tace Gwamnatin Tarayya za a cigaba da bi a hankali wajen cin bashin. Gwamnatin Buhari dai tace bashin da ta ci duk yana karewa ne wajen gina hanyoyin dogo da kuma tituna a kasar wanda za ayi shekaru 30 ana mora a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel