Shugabancin kasa a 2019: Sarakuna, da manyan Janar sun goyi bayan Tanimu, Tambuwal da Kwankwaso

Shugabancin kasa a 2019: Sarakuna, da manyan Janar sun goyi bayan Tanimu, Tambuwal da Kwankwaso

- Akwai yunkuri da wasu manyan yan siyasa ke yin a goyon bayan wasu yan takara a zaben shugaban kasa dake zuwa

- Wadannan manyan yan siyasa sun hada da sarakuna, manyan janarori da kuma wani tsohon shugaban kasar Najeriya

- Wasu daga cikin yan siyasan da suka samu wannan goyon baya sune; Aminu Tambuwal, Sanata Rabiu Kwankwaso da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman Turaki Tanimu

Yayinda ake shirye-shiryen zaben 2019, manyan masu ruwa da tsaki sunyi yunkurin nuna goyon bayansu ga yan takara uku daga yankin arewa maso yamma don ganin sun lashe kujerar shugabancin kasa.

Manyan yan siyasan na shirin goyon bayan wadannan shugabanni na arewa da suka hada da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Sanata Rabiu Kwankwaso da kuma wani tsohon ministan ayyuka na musamman, Turaki Tanimu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa goyon bayan ya na kokarin fadawa akan Tanimu koda dai Tambuwal da Kwankwaso sun kasance a fafutukar na dan wani lokaci yanzu.

Shugabancin kasa a 2019: Sarakuna, da manyan Janar sun goyi bayan Tanimu, Tambuwal da Kwankwaso

Shugabancin kasa a 2019: Sarakuna, da manyan Janar sun goyi bayan Tanimu, Tambuwal da Kwankwaso

An kuma tattaro cewa wasu manyan janar da suka hada da tsohon shugaban kasa Obasanjo da sarakuna da dama na wuyan sanata Kwankwaso domin ganin ya zamo shugaban kasa a 2019.

KU KARANTA KUMA: IMF: Za mu iya biyan duk bashin da ke kan mu – Ministar kudi

A halin yanzu Legit.ng ta rahoto a baya cewa shugabannin kungiyar matasan arewa sun shirya zaben gwaji ga wasu yan takarar shugabancin kasa daga Arewa.

Zaben gwajin zai kasance tsakanin shugab an kasa Muhammadu Buhari, Kwankwaso, Ahmed Makarfi, Sule Lamido, Tambuwal da kuma Dankwambo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel