Don na ceto Najeriya ba don bukatar kashin kai nake son zama shugaban kasa ba – Atiku

Don na ceto Najeriya ba don bukatar kashin kai nake son zama shugaban kasa ba – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babban burinsa idan ya zama shugaban kasa shi ne ya ceto Najeriya daga halin da take ciki, ba wai don bukatar kashin kai ne ba, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne a ranar Laraba 30 ga watan Mayu a yayin kaddamar da wata kungiyar yakin neman zaben Atiku, TAM-G da aka yi a jihar Legas, inda ya samu wakilcin shugaban kungiyoyin magayo bayan Atiku na kasa gaba daya, Oladimeji Fabiyi.

KU KARANTA: Kisan dan Achaba: Matasa sun kai farmaki ga ofishin Yansanda, sun babbaka Motoci

Atiku yace babban abinda zai sa a gaba idan ya zama shugaban kasa shi ne samar ma matasa ayyukan yi, sai kuma ya yi duk abinda zai iya don ganin ya hada kan yan Najeriya gaba daya, duba da yada ake samun rarrabuwar kai sakamakon bambancin addini da kabilanci.

Don na ceto Najeriya ba don bukatar kashin kai nake son zama shugaban kasa ba – Atiku

Atiku

“Bukatar ganin na bauta ma al’ummata da kwadayin ganin na habbaka tattalin arzikin Najeriya ta yadda zai amfani dukkanin yan Kasa ne ya sanya ni sha’awar sake tsayawa takarar shufgaban kasa, don haka takarata ba bukatar kai na bane, illa don ceto Najeriya.” Inji shi.

Wannan shi ne karo na biyar da Atiku Abubakar ke takarar shugaban kasa a Najeriya, daga karshe yace ba zai manta da mata ba, don haka ya bukaci da su mara masa baya, inda a cewarsa dole ne a baiwa mata hakkinsu da kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel