JOHESU sun bayyana dalilin janye yajin aikin da suka shafe kwanaki 44 suna yi

JOHESU sun bayyana dalilin janye yajin aikin da suka shafe kwanaki 44 suna yi

- Bayan shafe sama da wata daya suna yajin aiki yanzu haka an cimma matsayar wucin gadi

- Kafin cimma yarjejeniyar dai an kai ruwa rana sosai tsakanin JOHESU da likitoci

An cimma yarjejeniya a jiya domin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ma'aikatan asibitoci suka shafe tsawon kwanaki 44 suna yi.

JOHESU sun bayyana dalilin janye yajin aikin da suka shafe kwanaki 44 suna yi

JOHESU sun bayyana dalilin janye yajin aikin da suka shafe kwanaki 44 suna yi

Kungiyar jami’an lafiyan (JOHESU) ta bayyana cewa hakan ya biyon bayan sulhun da babbar Kotun ma’aikata ta kasa tayi a tsakanin bangarorin biyun.

Kafin zuwa yanzu dai wakilan kungiyar Kingdom Human Rights Foundation, wadda kungiya ce mai rajin kare hakkin dan Adam sun kai Kungiyar ta JOHESU kara kotu domin su dawo bakin aiki tare da kawon karshen yajin aikin da suka fara tun a ranar 21 ga wannan watan na Mayu 2018.

KU KARANTA: Jama’ar unguwa sun kai farmaki ofishin yan sanda, sun kona motarsu sanadiyar kisan dan achaba

Sai dai shugabancin wannan kungiya ya yi duba ga irin kiraye-kiraye da al’umma keyi da su dawo bakin aikinsu domin ceton rayuwar marasa lafiyar dake kwance a fadin asibitocin kasar nan. Zuwa yanzu dai kungiyar ta umarci ‘ya’yan kungiyar da su koma bakin aikinsu cikin awanni 24.

Mataimakin shugaban Kungiyar ta JOHESU, Dakta Chimele Ogbonna ya bayyanawa Jaridar Vanguard cewa “ A matsayinmu na ‘yan kasa na gari kuma kungiyarmu wadda tana girmama doka, yanzu haka zamu janye makaman yakinmu tare da dawowa bakin aiki a ranar 1 ga wata mai kamawa. Zamu yi hakan ne domin martaba darajar mutanen Najeriya, domin kungiyar mu kungiya ce mai neman zaman lafiya da kuma cigaban kowa da kowa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel