Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa shugaban kasar Sierra Leone

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa shugaban kasar Sierra Leone

A jiya Laraba ne a Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da sabon shugaban kasar Sierra Leone, Mista Julius Maada Bio, cewar Najeriya zata bawa kasar ta Sierra Leone goyon baya dari bisa dari don farfado da tattalin arzikin ta

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa shugaban kasar Sierra Leone

Abubuwan da shugaba Buhari ya fada wa shugaban kasar Sierra Leone

A jiya Laraba ne a Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da sabon shugaban kasar Sierra Leone, Mista Julius Maada Bio, cewar Najeriya zata bawa kasar ta Sierra Leone goyon baya dari bisa dari don farfado da tattalin arzikin ta.

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi shugaban kasar ta Sierra Leone a fadar shi dake Abuja, inda taya shi murnar nasarar da ya samu ta lashe zabe da kuma sabuwar gwamnatin da kasar ta samu.

DUBA WANNAN: Rarara zai wanke kanshi akan zargin da ake mishi

"Zamu cigaba da goyawa kasar ku baya domin ganin komi ya dai-daita. Mun san da cewa tabbatar da tsaro a kasashen Afirka dama duniya baki daya aikin mu ne gaba daya."

Yace Najeriya ta dade tana bayar da tallafin tsaro ga kasashe da dama, ballantana ma a shekara ta 11 na yakin basasa kuma zata cigaba da taimakawa gurin tabbatar da zaman lafiya da daidaituwar abubuwa domin samun cigaba baki daya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace akwai fannoni da yawa da suka yi kamanceceniya da shugaban kasar ta Sierra Leone, wanda suka hada da shugabantar kasashen su a lokacin mulkin soja, neman shugabancin kasar a jam'iyyar adawa kuma yaci tare da fuskantar kalubalen tsaro da durkushewar tattalin arziki.

A jawabin shugaban kasar Sierra Leone, yace kasar shi na godiya ga Najeriya sakamakon rawar da ta taka lokacin yakin basasa da kuma canjin da kasar ta samu a fannin siyasa tun daga lokacin.

Mista Bio yace zai yi duk abinda ya dace don ganin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tayi karfi, da kuma cigaba da dangantakar su da sauran kasashen duniya ta bangaren tsaro da cinikayya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel