Wata kwalekwale da aka dankara ma kaya ya nutse da mutane 20 da babura 9 a Ogun

Wata kwalekwale da aka dankara ma kaya ya nutse da mutane 20 da babura 9 a Ogun

Akalla mutane hudu ne sukarasa rayukansu sakamakon wata mummunan hatsari da ta rutsa da wasu fasinjojin wata kwale kwale a kauyen Akere na karamar hukumar Ipokia dake jihar Ogun, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu, da misalin karfe 11na safe, a yayin da kwale kwalen ke dauke da kaya, dalibai da sauran mutane zuwa tsallaken rafin, inda mutane da dama suka bace a sakamakon hatsarin.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Kotu ta kama wani tsohon gwamna da laifuka 6 da suka danganci karkatar da kudaden al’umma

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa nauyi da yayi ma kwale kwalen yawa ne ya musabbabin hatsarin, inda yace: “Kwale kwalen na duake da fasinjoji da suka hada da dalibai, buhuhunan Garri da dama, da kuma babura guda tara.”

Wata kwale kwale da aka dankara ma kaya ya nutse da mutane 20 da babura 9 a Ogun

Wata kwale kwale

Shugaban karmar hukumar Ipokia, Senayon Josu ya tabbatar da farwuwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutane hudu, yayin da mutane 10 suka tsallake rijiya da baya, bayan hadakar Yansandan ruwa, jami’an yansandan farin kaya da kuma masulta sun ceto su da kyar.

Daga karshe shugaban ya jajanta ma iyalan wadanda suka rasu a hatsarin, inda yace suna nan suna cigaba da kokarin ceto sauran mutanen da suka bace.

Shi ma Kaakakin runsunar Yansandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace rahoton da ya samu ya nuna cewa mutane uku ne kacal suka rasu, sa’annan ya kara da cewa zasu cigaba da kokarin ganin sun kwato sauran mutanen.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel