Wata mata ta sayar da gidan mijinta a bayan idonsa ba da izininsa ba

Wata mata ta sayar da gidan mijinta a bayan idonsa ba da izininsa ba

- Wata mata a Abuja ta sayar da gidan mijinta bisa yaudara a cewar zargin kotu

- Matar ta karyata zancen inda tace sharri ne kawai

- Kotu ta aika ta kurkuku na Suleja domin jiran hukumci

Wata mata ta sayar da gidan mijinta a bayan idonsa ba da izininsa ba

Wata mata ta sayar da gidan mijinta a bayan idonsa ba da izininsa ba

Wata mata a Abuja, mai suna Mrs. Ifeoma Ofuegbu, 'yar shekaru 41, ta fada hannu kotu bayan da mijinta ya zarge ta da sayar da gidan sa bisa yaudara da zamba, a bayan idonsa.

Sai dai ta karyata hakan, inda ta ce ita bata aikata laifi ko da daya ba, karya mijin nata yake mata.

Kotu ta ce a kaita gidan yari a garkame, zuwa lokacin da ake tsammanin karin bincike da kuma bayar da belinta.

Za'a kaita Suleja a tsare a kurkuku zuwa 13 ga Yuli, lokacin da za'a saurari bahasin bayar da belinta.

DUBA WANNAN: Daliba ta kashe miliyoyin kudi da ta tsinta a akawun dinta

Mai kai kara, lauya Hadiza Esai, tace matar ta sayar da gidan ne dake Dawaki a Abuja, kan kudi har N25m, sai dai nata lauyan yace sam matar bata yi wani laifi ba.

A dokar Najeriya dai, a tsarin mulki na 1999, babu yadda za'ayi wani cikin ma'aurata ya zagaye wani ya sayar da kadara ba tare da sahalewar dukkansu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel