Babu Alkawarin da na dauka yayin yakin neman Zabe a 2015 - Gwamna Bello

Babu Alkawarin da na dauka yayin yakin neman Zabe a 2015 - Gwamna Bello

A Yammacin ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewa ba bu alkawalin da ya yiwa al'ummar jihar sa a yayin da yake fafata yakinsa na neman zabe a shekarar 2015 da ta gabata.

Bello ya bayyana cewa, ya yanke shawarar sake neman takarar kujerar sa a zabe mai gabatowa na shekarar 2019 sakamakon mararin hakan da aka bayyana a gare sa na aikata hakan.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a fadar sa dake birnin Minna.

A kalaman sa, "babu alkawalin da na dauka yayin yakin neman zabe a 2015. Abu guda da muka tabbatar a yayin yakin neman zabe shine rashin daukarwa al'umma alkawali."

"Da ace mun dauki alkawali da mun fuskanci matsaloli da tsammanin al'umma sakamakon kalubalen da muka riska."

Babu Alkawarin da na dauka yayin yakin neman Zabe a 2015 - Gwamna Bello

Babu Alkawarin da na dauka yayin yakin neman Zabe a 2015 - Gwamna Bello

Bello yake cewa, tun kafuwar gwamnatin sa ta ke fuskantar kalubale musamman nakasun kudaden shiga da jihar sa ke samu daga asusun gwamnatin tarayya wanda ko Naira Biliyan 2 ba su haura ba.

KARANTA KUMA: Rayuka 2 sun salwanta a wani Hatsari a jihar Kano

Ya ci gaba da cewa, cikin yarda ta Ubangiji zai sake neman takara a shekara mai gabatowa karkashin jam'iyyar APC sakamakon bukatar da aka bayyana a gare sa.

A yayin haka ne gwamnan ya kirayi al'ummar jihar sa akan su fito su kada masa kuri'un su a zaben 2019 domin tabbatar da cikar manufofin da bai kai ga kammala su ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel