Gwamnatin Tarayya ta saki wani rahoto daga EFCC da tun mulkin Yar'aduwa aka yi shi

Gwamnatin Tarayya ta saki wani rahoto daga EFCC da tun mulkin Yar'aduwa aka yi shi

- Anyi bincike kan wutar lantarki da aka kashe wa makudan kudade

- An binciki tsohon shugaba Obasanjo ne amma ba'a same shi da laifi ba

- Kudaden da aka kashe basu kai $16b

Gwamnatin Tarayya ta saki wani rahoto daga EFCC da tun mulkin Yar'aduwa aka yi shi

Gwamnatin Tarayya ta saki wani rahoto daga EFCC da tun mulkin Yar'aduwa aka yi shi

Gwamnatin Tarayya ta saki rahoton EFCC kan aikin wutar lantarki wanda aka bincika ko an kashe dala biliyan shida kuma yaya aka yi dasu dazun nan.

MAtaimakin shugaban kasa Osinbajo shine ya saki rahoton, wanda tun zamanin Ummaru Yaraduwa aka hada shi, bayan dogon bincike kan wutar lantarki.

Bayanan, sun nuna yawan kudaden da aka rattaba a takarda, da ma iya kudaden da aka saki ga 'yan kwangila.

Ibrahim Lamorde, shugaban gudanarwar lokacin shine ya sanya wa rahoton hannu.

Rahoton bai ce shugaba Obasanjo na da hannu dumu-dumu kan sata ba, kamar yadda a lokuta da yawa ake zarginsa.

A kwanan nan shugaba Buhari ma yayi wannan shagube kan cewa an kashe biliyoyin daloli amma ba'a gani a kasa ba a wancan lokaci zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: Sharata shugaba Buhariu kawai yake yi

N10, 776,493,271:84; $69,808,942:70; Euros 12,853,883:40 da UKP8, 987,322:00 aka sakarwa 'yan kwangila a wancan lokaci kan shirin na NIPP wanda ya tarwatsa NEPA ya kuma sayar da kadarorinta ga 'yan kasuwa.

N11, 520,669,195:53; $375,435,687:37; da Euros7, 257,552:91 ce kuma aka sa rai za'a baiwa masu kwangilar a wancan lokacin.

Sai N1, 230,949,066,528:99 da aka ware don ci gaba da aikin inda kuma daga baya aka ake jiran sakin N360,714,147,700 da ma balas na N870,234,918,828 wanda za'a biya shima bayan kammala aikin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel