Dalilin da yasa Buhari ba zai fadi zaben 2019 ba – Fadar shugaban kasa

Dalilin da yasa Buhari ba zai fadi zaben 2019 ba – Fadar shugaban kasa

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya kafe kan cewar jam’iyyar APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zasu fadi zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Mohammed ya ce ba zasu fadi zaben 2019 ba saboda babu jam’iyyar da zata iya kayar das u tare da tambayar jam’iyyar da zata kayar da su zabe.

Ba zamu fadi zabe ba, wacce jam’iyya ce zata iya kayar da mu? Idan zamu yi aiki da zahiri, mun san babu adawa ta zahiri da zata iya kayar da mu zabe. Da a ce bamu tabuka komai ba a ofis sai na shiga fargabar zamu iya faduwa zabe,” a kalaman Mohammed.

Dalilin da yasa Buhari ba zai fadi zaben 2019 ba – Fadar shugaban kasa

Lai Mohammed

Mohammed ya yi alkawarin cewar zaben 2019 zai zama mai tsafta da tsari tare da cika bakin cewar gwamnatin Buhari na da abubuwan da zata yi yakin neman zabe da su.

DUBA WANNAN: Ambode da Buratai sun halarci bude wata barikin sojoji a Legas

Zamu yi yakin zabe da abubuwan da muka cimma na zahiri, wadanda jama’a ke iya gani. Misali, mun cika alkawarin da muka dauka a bangaren inganta tattalin arziki, yaki da ta’addanci da kuma cin hanci,” a cewar Mohammed.

Sannan ya kara da cewar, yanzu yankin arewa maso gabashin Najeriya, da a baya ‘yan ta’adda ke rike da wasu yankuna, yanzu ya samu dawowar zaman lafiya baya hawan Buhari da jam’iyyar APC mulkin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel