To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

- Wasu mazauna garin Maiduguri sun bayyana ra'ayinsu game da yunkurin da gwamnatin jihar take na tashin unguwar Galadima, saboda wajen ya yi kaurin-suna wajen saida kayan maye da kuma karuwanci da ake yi a wajen.

- Mabambantan ra'ayoyin dai ya nuna yadda wasu ke goyon baya yayin da wasu kuma ke sukar hukuncin

A wani rahoto da majiyarmu ta rawaito ya nuna cewa gwamnan jihar Kashim Shettima ya bawa mazauna yanki tsawon sati biyu da kowa ya bar yankin domin gwamnati zata rushe yankin baki daya, sai dai wannan yunkuri ya jawo cece-kuce. Gwamnan yace daukar wannan mataki ya zama wajibi domin gujewa sake aukuwar wani tashin hankali a nan gaba musamman idan aka yi duba da yadda rikicin Boko Haram ya jawo koma-baya ga jihar.

To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Bashir ya ce tashin wannan waje cigaba ne da kuma yin rigakafi da dukkan wani abu da iya zuwa nan gaba. Ya bayyana cewa duba da irin tashe-tashen hankula da aka fuskanta a shekarun da suka gabata a sakamakon rikicin Boko Haram, tabbas duk gwamnatin da ta san me take yi ta yi maganin irin wadannan gurare.

Jihar Borno ta tsinci kanta a cikin wani hali marar dadi wanda ya jawo asarar rayuka, dukiyoyi da kuma sauran abubuwan rayuwa na Biliyoyin kudi sanadiyyar rikicin Boko Haram. Abu ne mai wuya a maida asarar da aka yi nan da shekaru 5-7 masu zuwa. Kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.

Shi kuwa wani mazaunin yankin mai suna Danna, ya kalubalanci gwamnatin da cewa "Kamata yayi ace duk wani waje da aka san ana aikata miyagun ayyuka a rufe shi ba wai ace za a tashi anguwa baki daya ba saboda wasu tsirarun Mutane ba."

Sannan ya cigaba da cewa, "'Yan tada kayar baya na Boko Haram sun kashe dubban mutane, sun maida mata da yawa zawarawa tare da maida yara da dama marayu, wasu kuma sun zama nakasassu duk dalilin wannan rikici. Dan haka yanzu muna godiya ga Allah da ya dawo mana da zaman lafiya wanda hakan ne yasa har gwamnati tayi tunanin ganin ya kamata a tashi Galadima", Danna ya bayyana.

KU KARANTA: Hotunan Buratai da Ambode yayin bude wata sabuwar barikin sojoji a Legas

Shi kuwa Ali Bukar mazaunin Baga cewa ya yi "Abu ne mai kyau amma dalili kuwa shi ne zaka samu Bazawara bata da wanda zai iya kula da rayuwarta balle ta rayan da take da su, shi yasa wani lokacin suke fara harkar karuwanci saboda ita ce hanya mafi sauki da zasu iya samun abinda zasu ci sannan su kula da kansu."

Ya cigaba da cewa "Me kake tunani ga mace da ta zama baliga kuma babu wanda zai ke bata kudi ko kuma kula da ita, wannan shi ne dalili da yake jan hankalinsu domin fadawa sana'ar karuwanci. Ina mai fargabar idan har ba a yi wani abu wanda zai tallafi rayuwarsu ba, to, tabbas wannan al'amari zai zo mana har cikin gidajenmu."

To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

To fa! Kulle Gidajen Karuwai a Borno ya ya bar baya da kura

Shi kuwa Abubakar Suleiman cewa ya yi "Tashin wannan yanki babu wani abu da zai rage face bawa su masu wannan sana'a damar canja wani muhalli domin cigaba da abinda suke yi. Abu daya ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta nemo sahihiyar hanya tare da mafita wadda zata shigar da irin wadannan mutane a ciki wanda hakan ne kadai zai tallafi rayuwarsu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel