Hukumar Sojin Ruwa ta cafke Lita 386, 000 ta 'Danyen Man Fetur da Mutane 9 a garin Delta

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke Lita 386, 000 ta 'Danyen Man Fetur da Mutane 9 a garin Delta

Wani babban tarago dauke da lita 386, 000 ta danyen man fetur da mutane 9 da suka yo safarar sa sun shiga hannun hukumar sojin ruwa a jihar Delta.

Kwamandan rundunar reshen dake birnin Warri, Commodore Ibrahim Dewu, shine ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, inda yace an mika wannan mutane 9 da taragon su zuwa ga hannun hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC dake daura da barikin sojin.

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke Lita 386, 000 ta 'Danyen Man Fetur da Mutane 9 a garin Delta

Hukumar Sojin Ruwa ta cafke Lita 386, 000 ta 'Danyen Man Fetur da Mutane 9 a garin Delta

A yayin da yake jawabi bayan mika wannan mutane 9 da taragon su a hannun hukumar EFCC domin ci gaba da bincike, Commodore Dewu ya bayyana cewa sun damke su ne da laifin zuko man fetur din ta barauniyar hanya daga kamfanin Shell dake yankin Afremo.

KARANTA KUMA: Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna

Babban dakarun sojin ya yi gargadin cewa hukumar ba za ta gaza ba wajen dakile duk wasu masu ƙetare dokokin da ta gindaya, inda ya shawarci masu bukatar shiga kasuwancin man fetur akan aikata hakan ta hanyar da ta dace.

A nata bangaren, hukumar EFCC ta sha alwashin tsananta bincike akan mutanen da suka yi safarar man fetur kamar yadda jagoran wannan bincike Mista Richard Ogberagha ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel