Daliba ta ragargaji N365m da aka sanya a asusunta bisa kuskure kafin a ankare

Daliba ta ragargaji N365m da aka sanya a asusunta bisa kuskure kafin a ankare

- An sanya kudin ne har dala miliyan daya a asusunta maimakon 'yan canji don gudummawa

- A kasar Afirka ta kudu lamarin ya faru, kuma tuni an cafke ta

- Yanzu haka tana can tana fuskantar tuhuma bayan bushasha da ta tafka

Daliba ta ragargaji N365m da aka sanya a asusunta bisa kuskure kafin a ankare

Daliba ta ragargaji N365m da aka sanya a asusunta bisa kuskure kafin a ankare

A wani labari mai ban mamaki, dake fitowa daga kasar Afirka ta Kudu, an sami wata daliba da aka sanya wa akalla dala miliyan daya a asusunta na banki bisa kuskure, inda ake kokarin sanya mata 'yan daloli na tallafi da basu taka kara sun karya ba.

Sai dai maimakon ta maido wa da gwamnati kudin, $1.1m, Sibongile Mani, mai shekaru 28, daliba a jami'ar Walter Sisulu University da ke Eastern Cape province, wata jiha a kasar, kawai sai ta hau kashe kudinta inda har ta ci $63,000 daga kudin.

A cikin kudin dai, N40,000 ($110) ce kawai tata, agajin gwamnati ga dalibai marasa na hannu, amma kafin ma'aikatar da ta tura kudin ta ankare, tuni har ta sai waya, kayan sawa, ta kuma shirya casu da dalibai da abokai.

DUBA WANNAN: An kai kara don diyya kan raunin da aka yi wa Mo Salah

A ranar talata ne aka kamo budurwar aka kuma garzaya da ita kotun majistare don fuskantar hukuncin sata da almubazziranci, sai dai kamar ba'ayi uzuri ba, domin wa zai ga zunzurutun kudi daga gwamnati ya mayar mata?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel