Shema zai san makomarsa ranar 12 ga watan Yuli

Shema zai san makomarsa ranar 12 ga watan Yuli

- Tsofaffin masu Mulki musamman na jam'iyyar adawa na ganin takansu a yaki da cin hanci da rashawar da Gwamnatin APC ke yi

- Yanzu haka shi ma tsohon Gwamnan jihar Katsina da wasu Mutane makomarsa tana kasa tana dabo

A yau Laraba wata babbar Kotun dake sauraron karar tsohon Gwamnan Katsina kan badakalar Naira biliyan N11b da ake zarginsa da ita, ta dage shari’ar zuwa 12 ga watan Yuli domin bawa Lauyansa damar gamsar da Kotun rashin hannun tsohon Gwamnan kwamcalar.

Dage shari’ar dai ya biyo bayan damar Lauyan wanda ake kara (Shema) Joseph Daudu, SAN, ya nema don ya nazarci rahoton da aka gabatar wa kotun wanda ya nuna karara yadda tsohon Gwamanan ya yi almubazzaranci da N11b.

Shema zai san makomarsa ranar 12 ga watan Yuli

Shema zai san makomarsa ranar 12 ga watan Yuli

A cewar Mr Daudu sun sanya rai da karbar rahoton masu kara tun da dadewa amma sai a ranar 28 ga watan Mayu suka ji daga gare su wanda kuma ranar hutu ce, a don haka ne suke da bukatar samun wadataccen lokaci don nazarinsa sannan su gwada da nasu rahoton don su gano inda ke da matsalar.

KU KARANTA: Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

Amma sai dai lauyan masu kara (EFCC) Olatoke Olukayode SAN, ya musanta cewar basu bayar da rahotan da wuri ba, don a cewarsa tare suka bayar da kwafi ga Kotun da kuma wadanda ake karar.

Ya kuma kara da cewa rahotan ba shi da yawan da za’a daga shari’ar har zuwa lokaci mai tsawo.

Bayan kammala sauraren bangarorin biyu mai shari’a Ibrahim Bako ya dage zaman Kotun zuwa ranar 12 ga watan Yuli domin bawa Lauyan wanda ake kara damar bitar rahoton.

Ragowar Mutane biyun da ake tuhumarsu tare da tsohon Gwamnan sun hada da; tsohon kwamishinan kananan hukumomi Sani Makana da tsohon Sakataren ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Lawal Rufai da kuma wani shugaban kungiyar kananan hukumomi ta ALGON Lawal Dankaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel