Rayuka 2 sun salwanta a wani Hatsari a jihar Kano

Rayuka 2 sun salwanta a wani Hatsari a jihar Kano

Mun samu rahoton cewa a yammacin ranar Talatar da ta gabata ne kimanin rayukan mutane biyu suka salwanta yayin da mutane hudu suka raunata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a babbar hanyar birnin Kano zuwa garin Gwarzo.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana mun samu rahoton wannan hatsari ne da sanadin hukumar kwana-kwana ta jihar a ranar Larabar da ta gabata.

A yayin ganawa da manema labarai na NAN, Kakakin hukumar Mista Sa'idu Muhammad, ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne da misalin karfe 5.30 na yammacin ranar Talatar da ta gabata.

Rayuka 2 sun salwanta a wani Hatsari a jihar Kano

Rayuka 2 sun salwanta a wani Hatsari a jihar Kano

Hukumar ta samu rahoton wannan hatsari ne da sanadin wani Mallam Wada Alhassan, inda jami'an ta suka isa harabar wannan ibtila'i dake kan hanyar garin Gwarzo da misalin karfe 5.41 domin bayar da agaji na gaggawa.

KARANTA KUMA: Zaman da muka yi a Gidan Kaso ya daga daraja mu a nahiyyar Afirka - Orbih

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan hatsari ya afku ne a tsakanin wata babbar motar daukan kaya dauke da lambar XF 375 FG da kuma wata karamar mota kirar Golf mai lambar KZR 421 ZT.

Kakakin hukumar ya bayyana cewa wannan hatsari ya afku ne a sakamakon tsala gudu da ya sabawa ka'ida da direbobin motoci biyun ke yi a kan babbar hanyar.

Legit.ng ta fahimci cewa, an garzaya da fasinjojin motocin biyu zuwa asibitin Murtala Muhammad dake tantagwaryar birnin na Kano inda likitoci suka tabbatar da cikawar mutane biyu yayin da aka ci gaba da kulawa da wadanda suka jikkata.

A yayin haka Mista Sa'idu ya shawarci masu ababen hawa akan kiyaye ka'idoji da dokokin hanya domin zai taimaka kwarai da aniyya wajen takaita afkuwar hadurra.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel