Gwamnonin Jihohin APC za su yi yaki kan zaben Jam’iyyan da za ayi

Gwamnonin Jihohin APC za su yi yaki kan zaben Jam’iyyan da za ayi

Mun fahimci cewa a halin yanzu da ake shirin zaben shugabannin Jam’iyar APC wasu Gwamnonin Jam’iyyar mai mulki na samun sabani wajen wadanda za su maye gurbin shugabannin Jam’iyyar na kasa musamman a irin su Zamfara, Imo, da sauran Jihohi.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa wasu manya da Gwamnoni na Jam’iyyar APC na kokarin kakaba mutanen su a matsayin shugabannin Jam’iyyar na kasa. Yanzu haka dai Gwamnoni na kokarin ganin mutanen su ne su ka samu kujerun Jam'iyyar.

Kwanaki wasu a Jam’iyyar sun nufi Kotu inda su ka nemi a bar wadanda za su maye gurbin kujerun da za ayi takara su fito daga Yankin wadanda ke rike da mukaman a baya. Hakan ta sa ake ganin zai yi sauki Adams Oshiomole ya maye gurbin Oyegun.

Wasu Gwamnoni a APC dai na neman a bada dama a fito da shugabannin Jam’iyyar ba tare da bin yarjejeniyar kama-kamar da aka yi a baya domin su nada na su a kujerar su. A karshen wata mai zuwa ne dai za ayi zaben shugabannin Jam’iyyar na kasa.

KU KARANTA: Jiga-jigan APC da ke neman barin Jam'iyya sun hakikance kan batun su

Yanzu haka dai kujerar Sakataren Jam’iyya zai fito ne daga Yankin Arewa-maso-Gabas don haka ake kokarin rikici tsakanin Gwamnonin Borno da na Bauchi. Haka kuma manyan Jam’iyyar a Jihohin Arewa na harin kujerar Mataimakin Shugaban APC na kasa.

Gwamna Kashim Shettima yana bayan Maimala Buni a matsayin Sakateren Jam’iyyar. Sai dai kuma Gwamnan Adamawa da Gwamnan Bauchi ba su tare da Gwamnan na Borno. A Kano ma dai ‘Yan Kwankwasiyya da Ganduje za su buga wajen kujerar Ma’aji na kasa.

Haka kuma dai za a buga tsakanin Gwamna Abdulaziz Yari na Zamfara da Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai kan kujerar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar. Mutanen Kaduna dai sun fi so a maido kujerar zuwa Yankin su maimakon a maida shi zuwa Jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel