Yanzu yanzu: Kotu ta kama wani tsohon gwamna da laifuka 6 da suka danganci karkatar da kudaden al’umma

Yanzu yanzu: Kotu ta kama wani tsohon gwamna da laifuka 6 da suka danganci karkatar da kudaden al’umma

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja, ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da laifi guda shidda cikin tuhume tuhume 41 da EFCC ke kararsa akai, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar EFCC ta shigar da karar jolly Nyame ne kan wata badakalar kudi naira biliyan 1, da miliyan 64, gaban Alkalin Kotun, mai sharia Adebukola Banjoko, tun a shekarar 2007.

KU KARANTA: Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe

Wutar lantarki ta aika da wani mutumi lahira yayin da yake kokarin satar wayoyin lantarki

Jolly Nyame

Daga cikin laifukan da Alkali Banjoko ya bayyana kama Nyame ne da shi, akwai laifin karkatarwa tare da wawurar zambar kudi, wuri na guna wuri, naira miliyan dari biyu da hamsin, N250m, wanda ya bada umarnin fitar dasu ba tare da bin ka’idar kashe kudi a gwamnantance ba.

Ko a shekarr 2017, sai da wata Kotu ta kama Jolly da laifin yin sama da fadi da makudan kudade naira miliyan 250 da yayi ikirarin kashesu a wajen siyan littafai, takardu da biruka, don amfanin ofishinsa.

a wani labarin kuma, hukumar EFCC tace ta samu nasara akan barayi a gaban Kotu har sau 603, sa'annan ta kwato kudi sama da naira biliyan 500, a cikin shekarar 2018.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel