Babu batun Karin albashi a watan Satumba – Gwamnatin tarayya

Babu batun Karin albashi a watan Satumba – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa karin albashi mafi karancin ga ma'aikata ba zai samu ba a watan Satumba kamar yadda aka ruwaito tun da farko.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Ministan kwadago da Ayyukan yi Sanata Chris Ngige, ya bayyana cewa karin albashin ba zai yiwu ba saboda sai a karshen watan Satumba kwamitin da aka kafa ake sa ran zai kammala aikinsa.

Ya kara da cewa bayan kwamitin ya gabatar da rahotonsa, sai gwamnati ta duba ta tantance kafin ta yarda, daga nan sai ta tura ga majalisa.

Ministan ya kara da cewa iya biyan albashin, shi ne abu muhimmi game da karin albashin.

Babu batun Karin albashi a watan Satumba – Gwamnati tarayya

Babu batun Karin albashi a watan Satumba – Gwamnati tarayya

Ya ce aikin kwamitin ya shafi hadin kan ko wani bangarori da suka hada da jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu tare da saurarorin ra'ayoyin jama'a a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Bayan ganawa da Osinbajo, shugabannin nPDP sun ce lallai sai sun ga Buhari

A halin da ake ciki, Shugabannin sabuwar jam’iyyar PDP da suka koma APC zasu gana a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu domin sake duba ga makomar ganawarsu da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wani babban mamba na kungiyar ya bayyana cewa a ganawar da sukayi da Osinbajo kwanan nan, dole sai sun ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana korafinsu kai tsaye gare shi.

Rahoton ya kara da cewa Alhaji Kawu Baraje ya bayyana a Ilorin cewa kungiyar zata gana da Buhari bayan tattaunawa da mataimakin shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku bi shafukanmuna zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel