Bayan ganawa da Osinbajo, shugabannin nPDP sun ce lallai sai sun ga Buhari

Bayan ganawa da Osinbajo, shugabannin nPDP sun ce lallai sai sun ga Buhari

Shugabannin sabuwar jam’iyyar PDP da suka koma APC zasu gana a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu domin sake duba ga makomar ganawarsu da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Jaridar Punch ta rahoto cewa wani babban mamba na kungiyar ya bayyana cewa a ganawar da sukayi da Osinbajo kwanan nan, dole sai sun ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana korafinsu kai tsaye gare shi.

Rahoton ya kara da cewa Alhaji Kwau Barae ya bayyana a Ilorin cewa kungiyar zata gana da Buhari bayan tattaunawa da mataimakin shugaban kasa.

Bayan ganawa da Osinbajo, shugabannin nPDP sun ce lallai sai sun ga Buhari

Bayan ganawa da Osinbajo, shugabannin nPDP sun ce lallai sai sun ga Buhari

Sai dai rahoton yace yan sabuwar PDP basu samu ganawa da Buhari a ranar Litinin, 28 ga watan Mayu ba kamar yadda aka sanya rai saboda ayyukan da suka sha kan shugabna ksar wanda ya hade da bikin ranar dimokradiyya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

A halin da ake ciki, Sanata Dino Melaye ya bayyana sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel