Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

Sharudda hudu da 'yan nPDP suka gindayawa jam'iyyar APC

- Shari'ar shugaban majalisa Bukola Saraki yana daya daga cikin abubuwan da nPDP ke son jam'iyyar APC ta dakatar

- Sun kuma tabo batun ware kakakin majalisar wakilai Hon. Yakubu dogara daga taron gangamin jam'iyyar APC na jihar Bauchi

- nPDP kuma ta bukaci a kawo karshen abinda ta kira tursasawa da hukumar EFCC ke yiwa wasu daga cikinsu

Shuwagabannin sabuwar PDP wanda akafi sani da nPDP da suka fice daga jam'iyyar PDP suka dawo APC kafin shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2015 sun gindaya wasu sharudda muddin ana son su cigaba da zama a jam'iyyar ta APC.

Sun bayyana wadannan sharudda ne bayan ganawarsu da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a fadar Aso Villa a ranar Litinin 28 ga watan Mayu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kafa kwamitin mutane takwas don warware matsalolin da ke tasowa a tsakanin bangarorin biyu inda kowacce bangare za ta aike da mutane hudu.

KU KARANTA: Sultan ya yi kaca-kaca da wani gwamna da tsohon minista a kan alakanta kisan makiyaya da Danfodio

nPDP dai ta jima tana kukan cewa ana nuna mata wariyya musamman wajen bayar da mukamai duk da cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa jam'iyyar APC ta yi nasara a zaben na 2015.

Wasu daga cikin muhimman sharrudan da nPDP ta gindaya wa APC sun hada da:

1) Dakatar da shari'ar da ake yi wa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a kotun da'ar ma'aikata.

2) Kungiyar kuma tana bukatar a dena musgunawa kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a jihohinsu tare da basu guraben takara a zabukan fidda gwani a APC

3) Hukumar kuma tana bukatar a dakatar da binciken da hukumar EFCC ke yi wa wasu daga cikin su

4) Kungiyar har ila yau tana bukatar gwamnatin tarayya ta tsawata wa babban sufetan hukumar Yan sanda, Ibrahim Idris domin ya amsa gayyatar da majalisa ta yi masa don ya amsa tambayoyi game da wasu matsalolin tsaro.

Ana sa ran za'a warware matsalolin nan a zaman da za suyi na wata mai zuwa tare da tawagar shugaban kasa wanda ta kunshi mataimakin Ciyaman din APC, Lawal Shuaib, Alkalin Alkalai, Abubakar Malami, da mai bawa shugaba shawara a fanin tsaro, Babagana Munguno da kuma Ade Ipaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel