Cin Dunduniyar jam’iyya: APC zata dakatar da wani gwamna

Cin Dunduniyar jam’iyya: APC zata dakatar da wani gwamna

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a jihar Imo ya rubuta takardar neman kwamitin zartarwa na uwar jam’iyya ya a kan ya dauki mataki a kan gwamna Rochas Okorocha saboda cin dunduniyar jam’iyya.

Wannan batu na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC a jihar Imo, Mista Nwabueze Oguchienti, ya sakawa hannu.

Jawabin na Oguchienti ya ce, “bisa dogaro da sashe na 21D (11) na kundin tsarin jam’iyyar APC, kwamitin zartarwa na jihar Imo na neman uwar jam’iyya ta dakatar da gwamna Rochas Okorocha saboda aiyun cin dunduniyar jam’iyya da kan iya jawo karya dokokin jam’iyya a matakin jiha.”

Cin Dunduniyar jam’iyya: APC zata dakatar da wani gwamna

Rochgas Okorocha

Kazalika jawabin ya zargi gwamna Rochas da kafa shugabancin jam’iyyar APC a jihar Imo bayan kamala zaben shugabannin jihar da, Dakta Hilary Eke, ya lashe kujerar ciyaman. Sannan sun kara da cewar shugabancin Mista Chris Ogoma na cigaba da karbar takardu tare da bayar da takardun takara ga masu son fitowa a zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar.

DUBA WANNAN: Kotu ta yankewa tsohon gwamna Nyame hukunci shekaru 11 bayan gurfanar da shi

Kwamitin zartarwar jihar ya dakatar da Mista Chris Ogoma da Mista Obioma Ireagwu daga jam’iyyar bisa cin dunduniyar jam’iyya ta hanyar yiwa shugabancin jam’iyya na halak sojan gona tare da shawartar masu sha’awar tsayawa takara das u guji yin biyayya ga duk wani shugabancin jam’iyya a jihar wanda ba karkashin jagorancin Dakta Eke ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel