Tsautsayi: Wasu ‘Yan Bindiga dadi sun harbe ‘Yan sanda biyu har Lahira

Tsautsayi: Wasu ‘Yan Bindiga dadi sun harbe ‘Yan sanda biyu har Lahira

- Rayuka na cigaba da salwanta a kullum sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro a Najeriya

- Wani Kicibis da 'yan sanda su kayi ya zama ajalin biyu daga cikinsu

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe Jami'an 'yan sanda biyu har lahira a daidai mahadar Eliparawo kusa da titin Ada-George dake karamar hukumar Obio/Akpor a Jihar Rivers.

Wata majiya ta bayyana cewa 'yan bindigar sun bayyana ne a cikin wata mota baka kirar Jeep, daga bisani kuma suka afkawa jami'an 'yan sanda da harbi da misalin karfe 10:12pm na dare.

Tsautsayi: Wasu ‘Yan Bindiga dadi sun harbe ‘Yan sanda biyu har Lahira

Tsautsayi: Wasu ‘Yan Bindiga dadi sun harbe ‘Yan sanda biyu har Lahira

Wani mutum wanda lamarin ya auku akan idonsa mai suna Iyke yace, Jami'an tsaro guda biyu sun mutum a nan take yayin da guda daya kuma ya jikkata. Ya ce 'yan bindigar sun samu damar tserewa kafin jami'an tsaro sun bayyana a wurin da lamarin ya faru wanda a lokacin ake yunkurin kai wanda suka samu rauni Asibiti domin ceton rayukansu.

KU KARANTA: Dakarun sunyi wa wasu barayin danyen mai laga-laga bayan musayar wuta mai zafi

Ikye ya ce "Muna zaune ni da Abokaina a wajen shan kayan sanyi kawai sai muka hangi wata mota baka kirar Jeep ta sha gaban motar 'yan sanda, daga bisani kuma sai mu ka ji karar harbi, muna garzawa wajen sai muka tarar da 'yan sanda har mutum biyu da mutum guda daya kuma yana kwance cikin jini shi ne muka yi hanzarin kai sa asibiti, wannan shi ne iya abinda na gani da idona" Iyke ya bayyanawa manema labarai.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Rivers Nnamdi Omoni ya tabbatar da aukuwar wannan lamari sannan ya ce Jami'ansu har mutum biyu sun mutum, ya kara da cewa a yanzu haka sun gano motar mutanen da suka aikata wannan ta'asa kuma ya ce an baza Jami'an tsaro domin kamo su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel