Yanzu Yanzu: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Wani mamba na majalisar wakilai wanda ke wakiltan mazabar Kachia/Kagarko, Adams Jagaba ya sauya sheka daga APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

A wata wasikar da kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya karanto, dan majalisan daga jihar Kaduna ya bayyana rashin adalci da cigaba da dakatarwa daga jam’iyyar APC a matsayin dalilinsa na komawa PDP.

An tattaro cewa Mista Jagaba ya bar jam’iyyar APC bayan jam’iyyar ta sanar da dakatar dashi. Ya kuma bayyana APC a matsayin jirgin ruwa mai dilmiyewa.

Yanzu Yanzu: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Mista Jagaba ya kasance mutum na farko da sauya sheka zuwa PDP a majalisar wakilai a baya-bayan nan. Sauran duk da suka sauya sheka APC suke komawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye gidan gwamnatin Enugu saboda masu zanga-zanga

A halin da ake ciki, Sanata Dino Melaye ya bayyana sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel