Assha: Wasu 'yan uwa sun fyade wata mai tallar mangwaro

Assha: Wasu 'yan uwa sun fyade wata mai tallar mangwaro

Ana damke da wasu 'yan uwa biyu, Sani Mohammed da Ismaila bisa laifin aikata fyade ga wata yarinya mai tallar mangwaro a kauyen Madalla da ke karamar hukumar Suleja a jihar Neja.

A yayinda 'yan sanda sun damko Ismaila Mohammed, dan uwansa Sani Mohammed ya cika wandonsa da iska sai dai jami'an hukumar 'yan sandan Madalla sun bazama nemansa a halin yanzu.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, an gano cewa yan uwan biyu sun hada baki ne inda suka kira yarinyar da niyyar siyan mangwaro amma suka lalaba da ita cikin dakinsu inda suka yi mata fyade.

Assha: Wasu 'yan uwa sun fyade wata mai tallar mangwaro

Assha: Wasu 'yan uwa sun fyade wata mai tallar mangwaro

KU KARANTA: Fitattun jaruman Indiya 6 da suka taba ziyartar dakin Allah

Ismail ya shaidawa hukuma cewa tabbas sunyi wa yarinyar fyade.

"Mun yanke hukuncin yi mata fyade ne saboda babu kowa a gidanmu, munyi mata dabara har ta shigo dakinmu inda muka fada mata cewa zamu siye dukkan mangwaron amma sai mukayi lalata da ita," inji shi.

Ismail ya cigaba da magana cikin nadama inda ya ce, "Munyi nadamar abin da muka aikata ga yarinyar, muna fata iyayen mu za suyi mana gafara saboda mun shafawa sunan gidan mu kashin kaza."

Kakakin hukumar rundunar 'yan sandan, Muhammad Abubakar ya tabbatar wa al'umma cewa da sannu jami'an hukumar za su damko dayan wanda ake tuhumar don kara zurfafa bincike kana a gurfanar da su gaban kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel