Babu wani dalilin da zai sa a saka jam'iyyar APC da PDP a ma'auni guda - Osinbajo

Babu wani dalilin da zai sa a saka jam'iyyar APC da PDP a ma'auni guda - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu wata dalilin da zai sa a rika auna nasarorin jam'iyyar APC da na jami'iyyar adawa ta PDP.

Osinbajo ya ce wannan ya nuna cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta taka rawar gani sosai kenan idan har ma wasu na auna nasrorin ta da gwamnatin PDP da ta kwashe shekaru 16 tana mulki.

Mataimakin shugaban kasar ya furta wannan maganganu ne a jiya Talata yayin wata liyafar cin abinci da ake shirya a fadar Aso Villa don murnar ranar zagayowar demokradiyya.

Babu wani dalilin da zai sa a kwatanta jam'iyyar APC da PDP - Osinbajo

Babu wani dalilin da zai sa a kwatanta jam'iyyar APC da PDP - Osinbajo

KU KARANTA: Sultan ya yi kaca-kaca da wani gwamna da tsohon minista a kan alakanta kisan makiyaya da Danfodio

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi yan Najeriya albishir da ababan more rayuwa masu yawa daga gwamnati a yanzun da ake shiga shekara na hudu cikin mulkin shugaba Buhari.

"A halin yanzu da muka gab da shiga shekara ta hudu a wannan gwamnatin, akwai abubuwan alkhairi sosai da za'ayi wa al'umma," inji shi.

A cewar sakataren gwamnatin tarayyar, za'a dade ana tattauna a kan kasidar ranar zagayowar ranar demokradiya da tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega ya gabatar.

Ya ce: "Gaskiyar da Farfesa Jega ya tattauna a cikin kasidar abu ne da za'a dade ana tattaunawa a kai.

"Ya yi maganganu da dukkan bangarorin gwamnati, sashin zartarwa, sashin shari'a da sashin masu yin doka. Ya kamata su fara fada wa kanmu gaskiya har idan muna son canji ta gari."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel