Wani Fasto ya damfari dan cocinsa miliyoyin Naira

Wani Fasto ya damfari dan cocinsa miliyoyin Naira

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta kama wani Fasto shugaban cocin Jesus the General Outreach Ministry dake Amuwo-Odofin, jihar Lagas, ThankGod Udechukwu.

An kama Mista Udechukwu wanda ya fito daga Ozalla, karamar hukumar Awgu dake jihar Enugu sannan kuma yayi amfani da yarda da shi da daya daga cikin mabiyansa yayi a matsayinsa na ‘ma’aikin Allah’ ya kuma damfare shi a ranar 23 ga watan Mayu.

“Ni Fasto dinsa ne kuma bawan Allah. Nine ma nake yi mai addu’a don ya daukaka, ni nayi masa addu’a kafin ya tafi kasar Dubai,” cewarsa.

Faston yayi amfani da karya da kuma matsayinsa na limamin addini wajen damfarar wannan mabiyi nasa.

A cewar wanda aka damfara wanda ke zaune a kasar Dubai, ya fara fuskantar yaudara a hannun Mista Udechukwu da shawarar ya basa nmanyan motoci na Highlander Suv guda hudu da ya shigo da su, inda yayi ikirarin cewa daya daga cikin yan cocin zasi siya motocin wanda kudinsu ya kai naira miliyan 16.

Wani Fasto ya damfari dan cocinsa miliyoyin Naira

Wani Fasto ya damfari dan cocinsa miliyoyin Naira

Faston ya cire wasu kaso mafi yawa daga kudin inda yayi ikirarin cewa na dabaru ne. Sannan ya kawo shawarar fara harkar safarar mutane da kuma shawarar siyan motocin Sienna guda biyu. Sai kace yayi mun asiri, bayan na jira tsawon lokaci sai na sake amincewa da shawarar yin kasuwancin.

Har ila yau babu abun day a fito daga bangaren sufurin, sai mai korafin yace ya fasa yin kasuwancin inda ya bukacin faston ya saida motocin. An rahoto cewa Mista Udechukwu ya saida daya daga cikin motocin inda ya karkatar da kudin zuwa harkokin gabansa.

Yan watanni bayan haka, faston ya kara kawo shawarar kasuwanci ga mai karan inda ya gabatar das hi ga wani Chuks Amechi wanda yayi ikirarin yana aiki da wani kamfanin Najeriya kuma cewa zai taimake shi wajen yi masa hanyar da zai dunga kawo kaya ga kamfanin. Yayi ikirarin cewa hakan zai kai kimanin naira miliyan 2.37 wanda ya turawa asusun bankin kamfanin Mista Amechi da suna Royal Homes Furniture Company Limited a First Bank Plc.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Ba zan taba shiga harkar siyasa ba – Ali Nuhu

A lokacin da ya dawo gida Najeriya domin ya fara kasuwanci sai ya tarar da babu abunda ya saura daga hannun faston har abokinsa sunyi masa facaka da kudinsa wajen gudanar da harkokin gaban su.

Bincike ya nuna cewa yayi amfani da dukka kudaden wajen habbaka ginin coci da kuma harkokin gabansa.

Za’a mika lamarin zuwa kotu nan bada jimawa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel