An yi kaca-kaca da Buhari game da yaki da cin hanci da rashawa da yace yana yi

An yi kaca-kaca da Buhari game da yaki da cin hanci da rashawa da yace yana yi

Fitaccen dan siyasar na dake zaman tsohon dan majalisar wakilai da kuma majalisar dattijai kuma dan asalin jihar Kaduna, Sanata Baba-Ahmad ya yi kaca-kaca da kurarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na cewa tana yakar cin hanci da rashawa.

Sanatan a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Daily Trust ya bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasar ke wakar yana yi tamkar bita-da-kulli ne kawai domin cin zarafin wasu adawa da shi.

An yi kaca-kaca da Buharu game da yaki da cin hanci da rashawa da yace yana yi

An yi kaca-kaca da Buharu game da yaki da cin hanci da rashawa da yace yana yi

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya kafa tarihi 4 a duniyar tafsiri

Legit.ng ta samu cewa da aka tambaye shi kuma ko me yasa yake neman takarar shugaban kasa a 2019, sai tsohon Sanatan ya bayyana cewa yana neman ya zama shugaban kasar Najeriya ne domin ya bayar da gudummuwar sa ga cigaban kasar musamman ma yanzu da gwamnatin shugaba Buhari ta lalata ta.

A wani labarin kuma, Wani na hannun damar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai suna Injiniya Kailani Mohammed ya bayyana cewa su Saraki da Kwankwaso da ma dukkan 'yan tawagar su ta 'yan Sabuwar PDP wadanda suka koma jam'iyyar APC a gabanin zabukan 2015 sun riga sun gama yanke shawarar barin APC.

Sai dai kuma makusancin na shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa ficewar ta su daga jam'iyyar ta APC ba zata shafi kudurin tazarcen na shugaba Buhari a zaben 2019 ba domin kuwa talakawa na tare da shugaban kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel