Tura ta kai bango: Sarkin Musulmi ya yi kaca kaca da gwamnan jihar Benuwe da wani tsohon Minista

Tura ta kai bango: Sarkin Musulmi ya yi kaca kaca da gwamnan jihar Benuwe da wani tsohon Minista

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam dale karkashin jagonrancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III ta yi ma gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom wankin babban bargo game da zargin da yayi na cewa rikicin makiyaya da manoma na da alaka da jihadin Danfodio.

Shi dai gwamnan Benuwe ya yi zargin cewa Musulmai ne ke kokarin cigaba da jihad Dan Fodio ta hanyar fadada garuruwan da yaci yaki, don haka ne makiyaya suke kai ma manoma hari a jihar Benuwe, haka zalika shi ma tsohon ministan Obasanjo, Femi Fani Kayode ya yi wannan zargi.

KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu a wani arangama tsakanin yan bindiga da kauyawa Zamfara

Jaridar Punch ta ruwaito sakataren Jama’atu, Dakta Abubakar Khalid Aliyu yana gargadin gwamnan da ministan da su shiga taitayinsu, don kuwa Musulman Najeriya a kanwar lasa bane.

Tura ta kai bango: Sarkin Musulmi ya yi kaca kaca da gwamnan jihar Benuwe da wani tsohon Minista

Sarkin Musulmi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Khalid ya bayyana haka ne a yayin taron Jama’atu da ya gudana a babban ofishinta dake jihar Kaduna, inda yace akwai bukatar Musulmai su dage da addu’a don gudanar da zaben shekarar 2019 cikin kwanciyar hankali da lumana.

“Ina mayar da martani ne game da wani hira da gwamnan jihar Benuwe, Samuel Ortom ya yi, inda ya danganta rikicin makiyaya da manoma ga jihadin Shehu Usmanu Danfodio, cikin masu irin wannan zargin har da tsohon minista Femi Fani Kayode, don haka muna fada musu Musulunci bai yadda Musulmai su ci zarafin wasu mabiya addini ba, amma idan aka matsa musu ya zama wajibi mu kare kanmu.

“Da wannan ne muke gargadin gwamnatin jihar Benuwe da duk masu yin wannan zargi da cewa su shiga taitayinsu, don kuwa Musulman Najeriya ba kanwar lasa bane, don haka ba zamu lamunci cin mutunci ba, da yake kasar na fuskantar matsalar tsaro gami da cewa muna cikin wata mai alfarma, watan Azumin Ramadana, muna kira ga Musulmai da su kauda kansu game da ire iren zarge zargen nan, kuma mu kwantar da hankulanmu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel