Yan bindiga sun sace shanu, bindige mutane 3 har lahira a jihar Kaduna

Yan bindiga sun sace shanu, bindige mutane 3 har lahira a jihar Kaduna

Rundunar Yansandan jihar Kaduna ta tabbatar da kisan mutane uku tare da jikkata mutane hudu, wanda ake zargin wasu barayin shanu ne suka yi a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan harin ya faru ne a ranar Talata, 29 ga watan Mayu, a kauyen Kurega dake iyaka da karamar hukumar Birnin gwari a garin Chikun.

KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu a wani arangama tsakanin yan bindiga da kauyawa Zamfara

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya bayyana ma majiyarmu cewa yan bindigan sun kai farmakin ne da misalin karfe 2 na rana, inda yace sun yi awon gaba da shanu da dama, amma yansanda na kan bin sawunsu.

Yan bindiga sun sace shanu, bindige mutane 3 har lahira a jihar Kaduna

Yan bindiga

“Zuwa yanzu dai bamu kama kowa ba, amma muna iya bakin kokarinmu na ganin mun cafko dukkanin barayin tare da kwato shanun da suka sace, kuma sun kashe mutane uku sun raunata mutane hudu.” Inji shi.

Daga karshe ASP Aliyu ya shawarci jama’a mazauna yankin da su taimaka ta hanyar baiwa Yansandan muhimman bayanai da zasu iya kai ga kama barayin, kuma zasu cigaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel